Daga Yunusa Isa, Gombe

Wata Gobara data tashi da tsakar dare wayewar yau Litinin ta ƙona ɗaya daga cikin rumbunan magunguna na Ma’aikatar Lafiyar Jihar Gombe, lamarin da ya haddasa asarar magunguna da allurai da kayayyakin jinya na biliyoyin Naira.

Da yake zantawa da manema labarai yayin ziyarar ganewa idonsa abinda ya faru, Kwamishinan Lafiya na Jihar Dr Habu Ɗahiru yace gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare wayewar yau Litinin.

Yace “Ma’aikatan dake bakin aiki sun yi gaggawar sanar da jami’an dake kula da rumbunan, inda suma nan take suka sanar da ‘yan kwana-kwana don kai ɗaukin gaggawa, amma kafin ‘yan kwana-kwanan su isa, gobarar ta yi barna sosai, wanda har ya kai ga rugujewar katangar rumbun ta ɓarin gabas”.

Kwamishinan yace ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin gobarar da girman barnar da ta yi.

Ya ƙara da cewa, duk da lalata magungunan da za a yi amfani da su don rigakafin cutukan dake kashe yara a watan Maris mai zuwa kamar sanƙarau da Polio, gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da nasarar rigakafin.

Dokta Habu Ɗahiru yace ma’aikatar za ta gaggauta tuntuɓar Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin bada tallafi don cike giɓin da aka samu sanadiyyar gobarar.

A nasa ɓangaren, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Gombe wanda jami’in aikace-aikacen hukumar Umar Faruk ya wakilta, yace sun samu ƙiran waya na gaggawa da misalin ƙarfe 3:08 na dare, kuma nan take suka garzaya wurin.

Yace ‘yan kwana-kwanan sun samu nasarar shawo kan gobarar ta hanyar magance ci gaba da yaɗuwarta zuwa sauran sassan rumbunan.

Da yake zargin wutar lantarki da haddasa gobarar, jami’in kashe gobaran yace nan ba da daɗewa ba hukumar za ta yi wa manema labarai bayani idan ta kammala bincike.

Sai ya buƙaci ma’aikatu da hukumomi su riƙa horar da ma’aikatansu yadda za su yi amfani da kayayyakin kashe gobara yayin buƙatar gaggawa.

Har ya zuwa yammacin yau Litinin hayaƙi na ci gaba da tashi a wassu sassan rumbun.