Daga Yunusa Isa, Gombe

An ƙalubalanci Matasan Arewa Maso Gabas su riƙa bibiyar gwamnatoci don tabbatar da suna sauƙe nauyin daya rataya a wuyansu ta hanyar sanya ido da bin diddigin ayyukan zaɓaɓɓun shugabannin siyasa da waɗanda aka naɗa.

Wannan kalubalen ya fito ne ta bakin jagorar shirin YouthGovTracka ta Jihar Gombe Hadiya Usman yayin wani taron tattaunawa na shirin a Gombe.

Tace, “A matsayinmu na matasa, mun zo nan don tattaunawa kan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi ci gabanmu, ba a cika tafiya da mu a harkokin mulki ba, duk kuwa da cewa mu ne mafiya rinjaye a kusan kowace al’umma. Matasa ne ke zaɓan shugabanni a ko da yaushe, mu ne ke yanke shawarar shugabannin da za su mulke mu, mu ne a kan gaba wajen tantance sakamakon kowane zaɓe, kai ba zaɓe kaɗai ba, har ma da sauran al’amuran tattalin arziƙi da zamantakewa, mu ne muke jan ragama da kimanin kaso 70 cikin ɗari”.

Hadiya tace matasa su ne manyan masu ruwa da tsaki da ƙarfin da za su iya samar da kyakkyawar makoma ga ƴan baya masu zuwa, hakan yasa aka shirya taron don sanya ido da bibiyar gwamnatoci da shugabanni don tabbatar da suna sauƙe nauyin dake kansu.

Tace damawa da matasa a harkokin mulki yana ƙarfafa gaskiya da riƙon amana.

Da take tsokaci kan zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar a ranar 27 ga watan Afrilu mai zuwa, shugabar ta ƙarfafawa matasan gwiwa kan su fito kwansu da kwarkwata a fafata da su a zaɓen, ta hanyar tallafawa sabbin jini masu rajin samar da ci gaba daga tushe.

Hadiya ta kuma ja hankalin matasan su riƙa neman bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati don samun damar ganowa da ƙalailaice ayyukan gwamnati, don ganin ko sun dace da al’ƙauuran yaƙin neman zaɓe.

Ta jaddada cewa matasa ne kashin bayan duk wani ci gaba, don haka shirin na YouthGovTracka zai ci gaba da fafutukar ganin ana damawa da matasa a harkokin siyasa da mulki.

Da yake jawabi ga mahalarta taron su 100 daga jahohin Arewa Maso Gabas, shugaban shirin na Jihar Adamawa Riki Siman, yace “YouthGovTracka yana horar da matasa yadda za su riƙa gudanar da harkokin mulki da yadda za su riƙa bibiyar kasafin kudi da ayyukan gwamnatoci don ganin ko an yi su yadda ya dace ko kuwa”.

Yace shirin YouthGovTracka yana bincike tare da bankaɗo badaƙalar cin hanci da rashawa na gwamnatoci da jami’an gwamnati.

Riki yace shirin yana ƙarfafa damawa matasa da mata da naƙasassu wajen gudanar da mulki, yana mai cewa “a lokacin da jama’armu ke rike da madafun iko, zamu samu sauƙi wajen tsarawa da aiwatar da tsare-tsaren kyautata rayuwar nakasassu da mata da matasa.

Matasan da suka halarci taron daga sassa daban-daban, sun haɗa da ɗaliban manyan makarantu, da ƙungiyoyin fararen fula dana mata, da matasa masu hidimar ƙasa da naƙasassu da dai sauransu.

YouthGovTracka shiri ne da gidauniyar bunƙasa basirar matasa ta Brain Builders Youths Development Initiative ke daukar nauyi, tare da samun tallafi daga Youths Development Initiative, da Kungiyar Matasa Masu Fafutukar Demokraɗiyya Youth Democracy Cohort da kuma Tarayyar Turai.