Shugabannin Jam’iyyar APC reshen Jihar Gombe, sun dakatar da duk wani shirin ƴan siyasa masu sha’awar neman kujerar gwamnan jihar a 2027, tare da yin ƙira ga ɗokacin ‘ya’yan jam’iyyar su guji duk wani yunƙuri na yaƙin neman zaɓe ba bisa ƙa’ida ba, har sai an ɗage takunkumi kan haramcin yaƙin neman zaɓe.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar Ambasada Moses Kyari ya fitar a ƙarshen taron shugabannin jam’iyyar na Jiha, kuma ya miƙa ta ga Jewel Times Hausa.
Sanarwar tace bayan tattaunawa mai zurfi, jam’iyyar ta nuna matuƙar damuwa kan ci gaba da keta dokokin zaɓe da kundin tsarin mulkin jam’iyyar mai mulki da wasu ‘ya’yanta masu son tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2027 ke yi.
Jam’iyyar ta yi Allah-wadai da matakin da masu sha’awar takaran suke ɗauka, inda ta buƙacesu su guji ɗauke hankalin gwamnatin Inuwa Yahaya daga cika alkawuran yaƙin neman zaɓen data ɗaukarwa al’ummar jihar.
Don haka taron ya yanke shawarar dakatar da duk wani shiri da kwamitocin tuntuba da masu sha’awar takaran suka kafa, tare da jaddada aniyar tabbatar da bin wannan umarni sau da ƙafa, yana mai barazanar hukunta duk wani ɗan jam’iyyar da ya sabawa kundin tsarin mulkinta.
Haka kuma taron ya kaɗa kuri’ar gamsuwa da salon jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da nuna farin ciki kan irin nasarorin da ya samu saboda jajircewarsa wajen hidimtawa al’ummar Jihar Gombe don ci gabanta.