
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da korar Adamu Abdullahi Danko da wassu mataimaka uku nan take bayan binciken cin zarafin da aka yiwa Hon. Abdulrahman Abubakar Sheriff, Kansila mai wakiltar gundumar Shamaki a Ƙaramar Hukumar Gombe.
Wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarunsa Ismaila Uba Misilli ya fitar tace matakin wadda Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya sanar, ya biyo bayan kafa kwamitin bincike na musamman ne kan lamarin.
Sakamakon binciken kwamitin wanda rahotannin hukumomin tsaro suka tabbatar ne ya kai ga matakin da Gwamnan ya ɗauka.
A cewar Sakataren Gwamnatin Jihar, masu taimakawa gwamnan da abin ya shafa sune: Adamu Abdullahi Danko – Babban Mataimaki na Musamman na 2 kan Harkokin Cikin Gida, da Garba Mohammed Mai Rago – Babban Mataimaki na Musamman na 2 kan harkokin Siyasa, da Rabiu Sulaiman Abubakar – Babban Mataimaki na Musamman na 2 kan Kafafen Sada Zumunta na Zamani da kuma Ali Ibrahim Baban Kaya – Babban Mataimaki na Musamman na 2 kan Hulɗa da al’umma).
Gwamna Inuwa Yahaya ya bada umarnin cewa korar ta fara aiki ne nan take.
An kuma umurci duk jami’an da abin ya shafa su miƙa duk kadarorin gwamnati dake hannunsu ga hukumomin da suka dace ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci tashin hankali, rashin ɗa’a da cin zarafi ba, yana mai cewa ba zai lamunci duk abinda zai iya yin barazana ga zaman lafiyar jama’a ko lalata amincin da gwamnatinsa ke da shi a idon al’ummar jihar ba.
Ya tabbatarwa al’ummar Jihar Gombe jajircewar gwamnatinsa wajen bin doka da oda, riƙon amana da kuma zaman lafiya. Ya ƙara da cewa za a ɗauki matakai masu tsauri don kare zaman lafiya da ɗorewar kwanciyar hankalin da jihar take ta fafutukar ɗabbaƙawa.
