Daga Yunusa Isa, Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya sakamakon kamuwa da cutar sanƙarau da kuma wassu 5 da ake zargin suma sanƙarau ɗin ce ta kashe su.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr Habu Ɗahiru ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai kan ɓullar cutar ta sanƙarau a ƙananan hukumomin Nafaɗa da Funakaye.

Dokta Ɗahiru yace “Saɓanin jita-jitar da ake yaɗawa cewa gomman mutane sun mutu sakamakon wata shu’umar cutar da ba a tantance ba, binciken da masana lafiya na ma’aikatarmu da sauran ƙungiyoyin lafiya na ƙasa da ƙasa suka yi, da kuma sakamakon gwajin da muka tura sun tabbatar cewa mutum ɗaya ne kaɗai ya mutu sakamakon cutar ta sanƙarau a Ƙaramar Hukumar Funakaye, yayin da sauran biyar ɗin da suka mutu a Nafaɗa muke zargin cutar ce ta yi ajalinsu”.

Yace daga cikin mutane 95 da aka kai asibiti, an yiwa 84 jinya kuma an sallame su, yayinda aka ɗauki samfurin jinin mutane 29 da aka kai gwaji, inda 20 daga cikinsu suka dawo ba tare da wata cuta ba, 2 kuma aka tabbatar sun kamu da cutar ta sanƙarau, yayinda ake jiran sakamakon gwajin mutane 7, kana 6 kuma suna kwance a asibiti yanzu haka.

Kwamishinan yace tuni aka farfaɗo da tawagar kai ɗaukin gaggawa na jihar don sanya ido a dukkan sassan ƙananan hukumomin biyu don daƙile yaɗuwar cutar.

Yace “Ba za a iya ayyana matsalar a matsayin annobar sanƙarau ba, saboda ba a samu adadin mutanen da suka kai 10 ɗauke da cutar ba a cikin mutane 100,000 a mako guda”.

Sai dai yace an ɗauki matakan da suka haɗa da buɗe cibiyoyin kula da waɗanda ake zargin sun kamu da cutar, da fara gangamin wayar da kan sarakuna da malaman addini, da samar da magunguna da kayan aikin jinyar cutar kyauta don kula waɗanda ake zargin sun kamu, da kuma ɗiban samfurin jinin waɗanda ake zargin sun kamu don turawa ɗakunan gwaje-gwaje na Hukumar NCDC.

Dr Habu Ɗahiru ya shawarci al’ummar jihar su guji kwanciya a ɗakuna masu cunkoso musamman a irin wannan lokaci na zafi da cutar ta sanƙarau ta fi yaɗuwa.

Kwamishinan ya buƙaci al’ummar jihar su riƙa kwanciya a wuraren dake da wadataccen iska, sannan su hamzarta kai rahoton duk wani abu da suke zargi zuwa cibiyoyin lafiya mafi kusa.

Ya kuma gargaɗi jama’a su guji yaɗa jita-jita ko ɗaukan bayanan da ba a tantance ba dake fitowa daga waɗanda ba jami’an kiwon lafiya ba, musamman a shafukan sada zumunta na zamani.

Ya ƙara da cewa bisa cikakken goyon bayan da suke samu daga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ma’aikatar lafiyan jihar a shirye take ta magance duk wani ƙalubalen lafiya a jihar.