Daga Yunusa Isa, Gombe
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da kwamitin samar da matsaya mai mambobi 12 kan aiwatar da shawarwarin rahotannin kwamitin tsara birnin Gombe dana tantance harkokin kiwo, burtaloli da gandun daji.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da kwamitin a gidan gwamnati, gwamnan yace alhakin kwamitin sun haɗa da samar da tsarin aiwatar da shawarwarin rahotannin kwamitocin biyu da aka gabatarwa gwamnan a baya.
Haka kuma kwamitin zai baiwa gwamnatin jihar shawara kan yadda za ta yi amfani da shawarwarin don magance matsalolin tsara filaye da gine-gine a fadar jihar, tare da magance rikicin manoma da makiyaya da kuma zamanantar da harkokin kiwo a jihar.
Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ya wakilta, yace an zaɓo ‘yan kwamitin ne a tsanake bisa la’akari da irin ƙwarewa da gogewarsu a fannoni daban-daban na rayuwa.
A nasa ɓangaren, shugaban kwamitin samar da matsayar Aliyu Kamara, wadda tsohon shugaban ma’aikatan jihar ne, ya bada tabbacin sanya kwarewa da gogewarsu wajen baiwa gwamnati shawara kan yadda za a aiwatar da shawarwarin kwamitocin.
Ya buƙaci mambobin kwamitin su sadaukar da kansu don samun nasarar aikin da aka ɗora musu.
Kwamitin dai yana da makonni huɗu ya gudanar da aiki tare da miƙa rahotonsa.