Daga Yunusa Isa, Gombe

Hukumar Kiyaye Hatsurra ta Ƙasa (FRSC) Reshen Jihar Gombe, ta fara makon tunawa da waɗanda hatsura suka ritsa da su na 2024 da gudanar da taron wayar da kan jama’a a coci.

Da yake jawabi ga masu bi a Cocin Catholic Diocese na Saint Thereza dake Tumfure, Kwamandan Hukumar ta FRSC a Gombe Samson Ƙaura, yace magance hatsura alhaki ne na kowa da kowa.

“Hakan ne yasa hukumar FRSC ta ga ya dace ta yi amfani da wannar dama don jawo hankalin masu amfani da hanyoyi da hukumomin kula da hanyoyi su rungumi tsare-tsare masu aminci wajen amfani da hanyoyi. Muna ƙira ga gwamnatoci da hukumomi su inganta lafiyar hanyoyi ta hanyar bin tsarin fata lafiya nama lafiya wato ‘Safe System Approach’, muna kuma ƙira ga masu ababen hawa, da masu tafiyar ƙafa da sauran masu amfani da hanyoyi su gane cewa hatsuran ababen hawa suna kashe fasinjoji fiye da direbobi, don haka akwai buƙatar mu tuna cewa kiyaye hatsura nauyi ne na kowa da kowa. Muna ƙiran a yi biyayya ga duk dokokin zirga-zirga akan hanyoyin mu”.

Yace hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta don ganin ba a samu mace-mace ba sanadiyyar ababen hawa, ta hanyar shirya gangamin canza ɗabi’u don tabbatar da bin ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa kama daga direbobi, da masu tuƙa keke napep da jega, da masu babura da kekuna da sauran jama’a a yayin shagulgulan ƙarshen shekara.

Da yake magana game da ƙididdigar hatsura na 2023 da 2024, kwamandan yace “An fi samun aukuwar hatsura a Afirka, musamman ma Najeriya, yana mai cewa a bara, jimillar mutane 5,081 ne suka mutu yayin da wasu 31,874 suka jikkata a hatsura 10,617. Daga watan Janairu zuwa Satumban 2024 kuwa, jimillar mutane 3,767 ne suka mutu a cikin hatsura 7,011, kana mutane 22,373 suka jikkata”.

Da yake ƙira ga shugabannin addini dana al’umma da sarakuna su riƙa faɗakar da al’ummarsu kan illolin tuƙin ganganci, da kuma muhimmancin kiyaye ka’idojin zirga-zirga, Ƙaura ya ba da tabbacin ci gaba da haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki don samun sauyin tunani, da nufin kyautata yanayin zirga-zirgar ababen hawa a Jihar Gombe da Najeriya.

Da yake tsokaci, paston cocin na Katolika na Saint Theresa Diocese Bauchi dake Tumfure, Very Father Hillary Longs ya yabawa Hukumar ta FRSC bisa jajircewarta wajen rage hatsura a Jihar Gombe da Najeriya.

Ya yi ƙira ga gwamnatoci a dukkan matakai su gyara hanyoyi masu ramuka da kwazazzabai don ceton rayuka da dukiyoyin al’ummah.

Da yake ƙira ga masu bi su kasance masu bin doka da oda ba kawai a kan hanyoyi ba, paston ya ba da tabbacin yin amfani da tasirinsa wajen sauya tunani da ɗabi’un mabiya don ci gaban ƙasa.

An gudanar da addu’o’i na musamman don tunawa da waɗanda hatsura suka ritsa da su, tare da fatan Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma bada lafiya ga waɗanda suka jikkata.

Za kuma a yi makamancin waɗannan addu’o’i a masallatai ranar Juma’a mai zuwa.

Bikin tunawa da makon waɗanda hatsuran suka shafa na 2024 da hukumar ta FRSC ke gudanarwa, ta fara shi ne jiya Lahadi 17 har zuwa 23 ga wannan wata na Nuwamba, inda aka yiwa makon na bana taken “Wannar Ranar”.