Daga Yunusa Isa, Gombe
Ƙungiyar ci gaban gundumar Shamaki wato Shamaki Development Initiative Forum (SDIF) ta shirya bikin karrama ’ya’yanta maza da mata da suka yi fice wajen hidimtawa Shamaki da al’ummarta.
Da yake jawabi a yayin bikin a sabon babban ɗakin taro na Jami’ar Jihar Gombe jiya Lahadi, shugaban ƙungiyar Malam Musa Adamu, yace a karon farko an zaɓo mutane 11 ne da suka yi fice a anguwar don karrama su, domin nuna godiya da irin gudunmawar da suka bayar na musamman ga ci gaban Shamaki.
Yace waɗanda aka karraman sun fito ne daga sassa daban-daban na rayuwa, biyo bayan sanya ido sosai a kan irin gudunmawar da suke bayarwa, don haka ta yanke shawarar ƙarfafa musu gwiwa, don su zama abin koyi don wasu su yi koyi da su.
Shugaban yace ƙungiyar ta faro ne a matsayin ta abokai don tallafawa juna a shekara ta 2010, kana daga bisani ta faɗaɗa ayyukanta ga al’umma gundumar baki daya.
Yace “ƙungiyar Shamaki Development Initiative Forum ta samar da daruruwan guraben aikin yi ga matasanmu, mun bada tallafin karatu ga dalibai, da tallafin marayu da marasa galihu da dai sauransu”.
Musa ya ƙara da cewa wannar karramawa yanzu aka fara, domin akwai wasu ɗaruruwan `yan Shamaki da suka cancanci karramawa.
Waɗanda suka samu lambobin yabon sun hada da Alhaji Usman Adamu Turaki, tsohon kwanturolan hukumar kwastam ta Najeriya, da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Aihaji Adamu Damji, da babban daraktan asibitin koyarwa na tarayya FMC Gombe Dr. Yusuf M. Abdullahi, da Manajan kamfanin Em-One Energy Solutions Abubakar Gidado, da kwamishinan ma’aikatar kimiyya da kirkire-kirkire ta Jihar Gombe Farfesa Abdullahi Bappah Ahmed, da Kwamishina a Hukumar Kula Da Ma’aikata ta Gwamnatin Tarayya Dakta Ibrahim Jalo Daudu, da shugaban kolejin kimiyar magunguna ta Jami’ar Jihar Gombe Farfesa Muhammad Muhammad Manga, da Manaja gidan man Total Filling Station Gombe Alhaji Bappah Abubakar, da Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina J. Mohammed, da Major General MB Wabili da kuma karramawa ta bayan rai ga Babban Hakimin Gombe Marigayi Alhaji Abdulkadir Abubakar (Yariman Gombe).
A nasa jawabin shugaban taron kuma shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe Barista Sani Ahmad Haruna wanda mataimakinsa Muhammad Adamu Manga ya wakilta ya buƙaci ‘yan kungiyar su haɗa kai don samun nasarar ƙungiyar.
Uban taron Alhaji Usman Mohammad (Shamakin Gornbe) ya yabawa ’yan ƙungiyar bisa hangen nesansu, yana mai ba su tabbacin cikakken goyon baya da hadin kansu a kodayaushe.
A jawabin godiya a madadin waɗanda aka karraman, Alhaji Usman Adamu Turaki, ya yabawa kungiyar da suka ga abin da ya bayyana a matsayin ɗan gudunmawan da suke baiwa al’umma, yana mai bada tabbacin ci gaba da irin waɗannan ayyuka na alheri.
A nasa jawabin, babban baƙo na musamman Kadi Abdullahi Maikano Usman, ya yabawa ƙungiyar bisa jajircewarsu ga ci gaban Shamaki, inda ya shawarcesu da su ruɓanya ƙoƙari da kuma jajircewa ga addu’o’i don samun nasarar wannan taro.
Kadi Maikano Usman wanda daya ne daga cikin iyayen ƙungiyar, ya baiwa kungiyar tabbacin himmatuwarsu na ci gaba da mara musu baya a ko da yaushe.