Daga Yunusa Isa, Gombe

A ƙoƙarinta na magance hatsura a watannin ƙarshen shekara, Hukumar Kiyaye Hatsura ta Ƙasa (FRSC) Reshen Jihar Gombe, ta yi ƙira ga fasinjoji su guji yin shiru yayin da direbobi ke yi musu tukin ganganci don ceton rayuka da dukiyoyi.

Kwamandan hukumar a Jihar Gombe Samson Ƙaura ne ya yi wannan ƙiran yayin da yake ƙaddamar da gangamin magance hatsura a watannin ƙarshen shekara na bana, mai taken “Yi Magana Kan Tuƙin Ganganci: Hatsura Sun Fi Kashe Fasinjoji Fiye Da Direbobi”.

Yace, “A matsayinmu na jami’an wannar hukuma, yana da kyau mu haɗa kai da masu ababen hawa, don nuna musu ka’idojin hanya dana tuƙi, da yadda za su kai rahoton tuƙin ganganci, da amfani da ɗamarar tuƙi, da kuma gujewa tuƙin ganganci. Wajibi ne fasinjoji su guji duk abinda zai ɗauke hankalin direba, kana su bada gudummawar da za ta kyautata yanayin tuƙi, a mafi yawan lokuta, hatsura sun fi illa ga fasinjoji akan direbobi, don haka akwai buƙatar su riƙa magana a duk lokacin da suka ga ana tuƙin ganganci”.

Yace hukumar ta sake bitar dabarunta na wayar da kan jama’a don ƙarfafa gwiwar fasinjoji su san haƙƙinsu na daƙile tuƙin wuce gona da iri da direbobin ke yi, “Saboda alƙaluma sun tabbatar da cewa fasinjoji sun fi mutuwa a yayin hatsura fiye da direbobi, don haka akwai buƙatar su riƙa sanya ido sosai ga direbobi a yayin tuƙi”, a cewar kwamandan.

Kwamandan hukumar kiyaye hatsuran yace gangancin direbobi da halin ko-in-kula na fasinjoji a yayin tuƙi, suna daga cikin abubuwan dake haifar da ƙaruwar hatsura a Najeriya.

Ƙaura ya ƙara da cewa don rage yawan hatsura akan hanyoyi, hukumar ta shirya gangamin wayar da kan fasinjoji da sauran masu ruwa da tsaki a yayin gangaminta na wayar da kan jama’a.

“Don aiwatar da wannan tsari, mun mai da hankali kan sake wayar da kan fasinjoji, tare da taimaka musu su fahimci haƙƙoƙinsu. Amanar dake tsakanin direba da fasinja a bayyane take: cewa dole ne direba ya tabbatar ya isar da fasinjoji inda za su je cikin ƙoshin lafiya ba tare da an tauye musu haƙƙinsu ko ji musu rauni ko kashe su ba, ta hanyar ƙarfafa fasinjoji ne za mu rage yawan hatsuran ababen hawa”.

Da yake ƙiran a haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin masu ruwa da tsaki don daƙile wannar matsala, kwamandan hukumar yace sakamakon irin matakan da hukumar ta FRSC ke ɗauka, an samu raguwar hatsura da kaso 5 cikin ɗari daga rubu’in farko zuwa rubu’i uku na wannar shekara idan aka kwatanta da na bara.