Labarin dake shigo mana da ɗumiɗuminsa daga hukumar tsaro ta Civil Defence na cewa kwamandan hukumar tsaro ta Civil Defence Reshen Jihar Gombe Muhammad Bello Muazu, ya jaddada ƙudurin rundunar na fatattakar ɓata gari da masu aikata miyagun laifuka a anguwar Tumfure dama Jihar Gombe baki ɗaya.
A wata sanarwa ta musamman da ya miƙawa Jewel Times Hausa da yammacin yau, kwamandan yace, rundunar ta lura cewa munanan dabi’u suna sake ɓullowa a anguwar, lamarin da ya sabawa doka da al’adun al’ummar Jihar Gombe.
Bello Muazu yace “Rundunar Civil Defence za ta fara sintiri na musamman a Anguwar Tumfure daga yau Laraba, muna shawartar jama’a su rufe wuraren kasuwancinsu daga karfe 10:00 na dare domin sintirin jami’anmu ya gudana cikin nasara, kuma jama’a su kaucewa jefa kansu cikin matsala, Civil Defence ba ta da niyyar musgunawa kowa”.
Kwamandan na Civil Defence na jihar ya nemi goyon baya da haɗin kan sarakuna da shugabannin al’umma da kuma mazauna anguwar ta Tumfure don samun nasarar fatattakar masu aikata laifuka dake yankin.
Muhammad Bello Muazu ya ƙara da cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen magance duk wani da aka samu da yiwa doka ƙaran tsaye.