Daga Yunusa Isa, Gombe

Shirin Samar Da Hanyoyi Da Bunƙasa Kasuwanci a Yankunan Karkara (RAAMP), ya buɗe kashi na biyu na neman kwangilolin hanyoyin karkara guda uku a ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Gombe masu tsawon kilomita 74.96.

Da yake jawabi yayin buɗe buƙatar neman kwangilolin, Kodinetan shirin na RAAMP na Jihar Gombe Injiniya Salisu Abdullahi, yace shirin na da nufin inganta rayuwar al’ummomin yankunan karkara ne ta hanyar samar da hanyoyi masu inganci dake haɗe ƙauyuka da kasuwanni da garuruwa dama birane.

Ko’odinetan yace “Hanyoyin da za a yi sune Hanyar Sharfuri zuwa Magaba a Ƙaramar Hukumar Funakaye, da Hanyar Kembu zuwa Kidda zuwa Panda a Ƙaramar Hukumar Akko, sai Hanyar Daniya zuwa Daban Fulani a Ƙaramar Hukumar Kwami da kuma Hanyar Dukku zuwa Zange a Ƙaramar Hukumar Dukku”.

Yace kwamitin tantancewa zai yi nazari sosai kan buƙatun da kamfanoni 12 dake neman kwangilolin suka gabatar, yana mai bada tabbacin cewa za a samu waɗanda za su yi nasara bayan kammala tantancewar.

Ko’odinetan ya baiwa masu neman kwangilolin tabbacin yin adalci da gaskiya a yayin aikin tantancewar.

Injiniya Salisu ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa jajircewarsa wajen samar da ababen more rayuwa a karkara da kuma samar da ribar dimokuradiyya ga ‘yan ƙasa.

A nasa jawabin Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na jihar Injiniya Maijama’a Kallamu wanda Daraktan Gudanarwa da Kuɗi Abubakar Ibrahim Lamuwa ya wakilta, ya buƙaci kamfanonin su kasance masu bin ƙa’ida wajen gudanar da ayyukansu.

Kwamishinan ya yabawa shirin na RAAMP bisa nuna gaskiya da adalci wajen karɓar buƙatun kamfanonin, yana mai ƙira garesu su riƙa gudanar da ayyuka masu inganci tare da kammalasu akan kari.

Da yake jawabi a madadin kamfanonin da suke neman kwangilolin, Abdulmajid Muhammad daga Kamfanin J.M & S Constructions ya yaba da yadda aka karɓi buƙatun nasu cikin gaskiya da adalci, yana mai tabbatar da cewa idan kamfaninsa ya yi nasara, zai gudanar da aiki mai inganci kuma a kan kari.