Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe, CP Hayatu Usman ya fita sintiri na musamman a kananan hukumomin Kaltungo da Billiri.

A cewar wata sanarwar mai dauke da sanya hannun mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Asp Sharif Sa’ad, CP Hayatu Usman ya kai ziyarar gani da ido a hedikwatar ‘yan sanda ta Kaltungo da Billiri a yayin sintirin.

Sintirin yana daya daga cikin kokarin da Kwamishinan ya ke yi na inganta tsaro da rayuka da dukiyoyi a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake gudanar da aiki a hedikwatar ‘yan sandan na Kaltungo da Billiri. Ya yabawa dakaru da jami’an sashin bisa jajircewarsu wajen gudanar da aiki, ya kuma bukacesu su ci gaba da wannan kokari.

CP Hayatu Usman ya jaddada kudirin rundunar ‘yan sandan jihar na hada kai da sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki wajen yaki da miyagun laifuka, tare da tabbatar da zaman lafiyan al’umma.

A yayin ziyarar tasa, CP Hayatu Usman ya tattauna da jami’an ‘yan sanda na kananan hukumomin biyu wato DPOn Billiri, CSP Ahmed Sanda, dana Kaltungo CSP Paul Pama, inda suka yi wa kwamishinan ‘yan sandan karin bayani kan sha’anin tsaro a yankunansu.

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe karkashin jagorancin CP Hayatu Usman, ta kama wassu mutane biyu da ake zargi da laifin hadin baki da algus din kayan abinci musamman shinkafa.

A cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da sanya hannun mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Asp Sharif Sa’ad, wadanda ake zargin sun hada da Bashir Haruna mai shekaru 35 na anguwar Dubai Quarters a Gombe da kuma Muhammed Isa mai shekaru 54 daga anguwar Jibilu dake Kumo a karamar hukumar Akko.A cewar sanarwar, wadanda ake zargin da aka kama a ranar 24 ga wannan watan bisa samunsu da gurbatattun buhunan shinkafa 57 da aka yiwa algus da nufin sayarwa jama’a a matsayin shinkafa mai kyau.

Don haka kwamishinan yan sandan CP Hayatu Usman ya shawarci al’umma su yi hattara da irin wadannan masu aikata miyagun laifuka, sannan su rika lura da irin hatsin da suke saya a buhuna don gudun fadawa tarkon irin wadannan yan damfara.

Rundunar ta tabbatarwa al’ummar jihar cewa ‘yan sanda a jihar Gombe za su ci gaba da jajircewa wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma tabbatar da bin doka da oda, tana mai cewa da zarar ta kammala bincike zata gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.