Daga Yunusa Isa, Gombe

 

Jam’iyyar PDP a Gundumar Kumo Gabas dake Ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe, ta sanar da korar Dr. Bashir Abdullahi (Gaddafi) bisa zarginsa da ɗaukar nauyin ’yan daba don tarwatsa taron manyan jami’an jam’iyyar a Gombe.

Da yake zantawa da Jewel Times, Shugaban Jam’iyyar PDP na Kumo Gabas, Amadu Sule, yace jam’iyyar ta gaji da irin ta’asar da Gaddafi ke yi, lamarinda yace ya sabawa manufofin jam’iyyar na samar da zaman lafiya da ci gaba.

“A bisa ƙa’idoji da manufofinmu, duk wanda ya yiwa manyanmu ba daidai ba, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar tsattsauran mataki akansa, wannan ba shi ne karon farko da Gaddafi yake saɓa dokokin jam’iyyarmu ba, amma ana yi masa afuwa, a wannan karon ya kai mu har bango, ganin yadda yasa ’yan kalare ɗauke da makami su kai hari, da muzgunawa, da kuma tsoratar da dattawa da jami’ai da ‘ya’yan jam’iyyarmu, ba za mu lamunci ta’addancin da yake yi a jam’iyyar PDP ba, don haka a bisa ga ikon da aka ba ni a matsayin shugaban jam’iyya na Kumo ta Gabas, mun kori Gaddafi daga jam’iyyarmu ta PDP kuma ba ma bukatarsa a cikinta,” in ji Amadu.

Yace matakin ya zama dole ne don tabbatar da zaman lafiya ya wanzu a jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar ya ƙara da cewa, “Ba wai muna ƙyamarsa ba ne, sai dai ba za mu iya jurewa irin ta’asar da yake yi ba.”

Amadu yace jam’iyyar ta gargadi Gaddafi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba kan rashin mutuncin da yake yi a cikinta, inda yace ba za su lamunci wani laifi na uku ba daga gareshi. Don haka suka yanke shawarar korar shi.

Ya ƙara da cewa, “Ni ne na fi kusa da shi a jam’iyyar PDP, amma tunda ya yanke shawarar tada hankula, ba ni da wani zaɓi illa bin ka’idojin jam’iyya da kuma yin abin da ya dace.

Da yake bayyana cewa babu wanda ya taba aikata irin wannan ta’asa a PDPn Akko, shugaban jam’iyyar na Kumo Gabas ya ja kunnen sauran ‘ya’yan jam’iyyar da su guji tayar da rikici a cikinta.

Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani ɗanta da ya saɓawa ka’idojinta.

Wani ganau, Muhammad Jalige, ya shaidawa Jewel Times cewa, “Gaddafi ya ɗauki nauyin yan kalare fiye da 20 ɗauke da sanduna, adduna, da wukake, inda suka far wa dattawa da jami’an jam’iyyarmu a wurin taron, suka lalata dukiyoyi, tare da sace wassu abubuwan na mahalarta taron, ciki har da shinkafa,” in ji shi.

Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin Gaddafi ya ci tura, kasancewar wayarsa bata shiga, kuma bai amsa saƙonnin da aka aike masa ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Amma wata kafar yaɗa labarai a jihar ta ruwaito Gaddafi yana bayyana ficewarsa daga jam’iyyar ta PDP.

Gaddafi dai shi ne ɗan takaran jam’iyyar a Akko ta Tsakiya a zaɓen 2023, inda ya zo na biyu bayan da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe Abubakar Muhammad Luggerewo na Jam’iyyar APC ya doke shi.

Bayan ayyana sakamakon zaɓen, Gaddafi ya ƙalubalanci nasarar Luggerewo a kotu, rikicin da ya ƙarƙare a babbar kotun tarayya.