Daga Yunusa Isa, Gombe

Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Gombe ta janye daga shiga zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi ranar Asabar ɗin nan.

Da yake jawabi a yayin gabatar da tutoci ga ‘yan takarar shugabancin ƙananan hukumomi da kansiloli a Gombe, Shugaban Jam’iyyar na Jiha Barista Rambi Ibrahim Ayala, yace NNPP ta yanke shawarar janye shiga zaɓen ne har sai an yi gyare-gyaren kundin tsarin mulki don baiwa ƙananan hukumomi yancin cin gashin kansu tare da baiwa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC damar gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.

Yace sun kuma yanke shawarar kin shiga zaɓen ne saboda wasu dalilai da ke nuna cewa jam’iyya mai mulki da hukumar zaɓe ta jihar ba su nuna ƙudurin gudanar da zaɓen a jihar ba.

Rambi ya yi zargin cewa jam’iyya mai mulki a wassu lokuta ta bayyana ƙarara cewa babu shakka ‘yan takararta ne za su lashe zaɓen.

A nasa jawabin jagoran jam’iyyar kuma ɗan takararta na gwamna a zaɓen 2023 Hon. Khamisu Ahmad Mailantarki, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa ganin yadda jam’iyyar take da cikakken tsarin shugabanci a faɗin gundumomi 114 na jihar, ko shakka babu NNPP ce za ta lashe zaɓen 2027.

Da yake ƙarfafawa ’yan jam’iyyar gwiwa kan haɗin kai, kishin ƙasa da jajircewa, Mailantarki ya ba da tabbacin cewa jam’iyyar na da kyakkyawan matsayi na kafa gwamnati mai zuwa a jihar.

Da yake jawabi a madadin ‘yan takaran da aka baiwa tuta, ɗan takaran shugaban karamar hukumar Gombe a jam’iyyar, Adamu Babale Makera, ya bayyana goyon baya ga matsayin jam’iyyar na kin shiga zaɓen.