Daga Yunusa Isa, Gombe

Shugabanni da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a Ƙaramar Hukumar Ɓillliri ta jihar Gombe, sun jaddada goyon baya da biyayyarsu ga jagorancin shugaban jam’iyyar na jiha Hon. Barista Rambi Ibrahim Ayala, tare da nuna gamsuwa da salon shugabancinsa.

Goyon bayan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar Bayan taro da sakataren jam’iyyar na shiyya Billy Garba Tal ya karanta, bayan wani babban taron shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Ɓilliri.

Da suke yabawa irin ƙoƙarin da Barista Rambi ke yi na farfaɗo da jam’iyyar NNPP a jihar, shugabannin jam’iyyar na Ɓilliri suka ce, “Wasu ƴan kwangilar siyasa da ba su da alaƙa da NNPP a wannar ƙaramar hukumar, suna ɗaukar da kansu a matsayin ‘ya’yan babbar jam’iyyarmu a Billiri, alhali suna aikin iyayen gidansu ne na jam’iyyun adawa, sun je sun fitar da wata sanarwar cin mutunci da ɓata suna a yunƙurinsu na shafa kashin kaji ga martabar shugaban jam’iyyarmu na jiha”.

“A cikin sanarwar ta su, waɗannan ‘yan kwangilan siyasa sun ƙare da yin ƙarya ta hanyar yin jabun sa hannun mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, don haka muna ƙira ga jami’an tsaro su gaggauta gudanar da bincike tare da gurfanar da Ambrose Ismaila Mairungu, da Amatiga Naboth da kuma Amuga Barde bisa wannan ɗanyen aiki,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa a ranar 26/02/ 2024, jam’iyyar a Ɓilliri ta dakatar da Ismaila Mairungu saboda yiwa jam’iyyar zangon ƙasa, da almubazzaranci da kuma rashin ɗa’a.

Sanarwar ta bada hujjar cewa “Don yin biyayya ga sashi na 30 na kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu, mun miƙa wannan batu ga kwamitin ladabtarwa don ɗaukan mataki na gaba, amma abin baƙin ciki sai Mairungu ya ƙi bayyana a gaban kwamitin, don haka ya kasance jam’iyyar ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta kore shi da abokan tafiyarsa baki ɗaya daga cikinta”.

Idan za a iya tunawa dai Amatiga Naboth da tawagarsa, a yayin wata ganawa da manema labarai kwanan nan a Gombe, suka kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da Rambi, suna masu zarginsa da ɗauki ɗoran shugabanci a jam’iyyar ta NNPP reshen Ɓilliri, inda suka yi ƙira ga uwar jam’iyyar ta ƙasa ta ɗauki matakin ɗaya kamata.

Sai dai a yayin taron na Ɓilliri, mahalarta sun nuna goyon bayansu ga sabin shugabannin NNPPn na ƙaramar hukumar ƙarƙashin jagorancin Hon. Yila Dankuka da shugabannin jam’iyyar na gundumomin ƙaramar hukumar guda 10, suna masu bayyana sabin shugabannin a matsayin alƙiblar da za ta kai NNPP ga nasara da ɗaukaka a ƙaramar hukumar.

Sanarwar bayan taron ta kuma buƙaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe (GOSIEC) ta tabbatar ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na gaskiya da adalci, tana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa demokraɗiyya a Jihar Gombe da Najeriya.

A saƙonninsu na fatan alheri, uban jam’iyyar a Ɓilliri Elder Victor Iliya, da ‘yar takarar shugabancin ƙaramar hukumar a NNPP Rose Simon, da dattijon jam’iyya Mista Kasina Elsa da kuma jami’in hulɗa da jama’a na NNPP na jiha Terry Ibrahim Yusuf, suka ce wassu daga waɗancan masu ƙiran kansu masu ruwa da tsaki na NNPP ba su da ƙwarin gwiwa da kishin Ɓilliri da jama’arta, don haka suka gudanar da taron manema labaran da suka yi a Gombe.

Suka ce wasunsu ma ba ’yan asalin Ƙaramar Hukumar Ɓilliri ba ne ko Jihar Gombe, don haka ba su da hurumin yanke shawara kan duk wani abu da ya shafi Ɓilliri a kowane irin matsayi.

Masu ruwa da tsakin suka ƙara da cewa an zaɓi sabin shugabannin NNPPn na Ɓillliri ne ta hanyar da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadar.

Da yake jawabi a madadin shugabannin NNPP na gundumomin ƙaramar hukumar ta Ɓillliri guda 10, shugaban jam’iyyar na gundumar Tudu-Kwaya Yusuf Ayayyafa, yace su masu bin doka da oda ne, hakan yasa suka amince, kuma suka yi biyayya ga Mairungu a lokacin da yake shugaban jam’iyyar na riƙo, kuma yanzu ma suna biyayya ga sabin shugabannin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya amince da su ƙarƙashin Hon. Yila Dankuka a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar.

Tun farko a nasu tsokaci, Yila Dankuka da mataimakinsa Hon. Nathan Kalfado, suka ce an baiwa Samaila Mairungu da sauransu damar su janye matsayarsu tare da neman afuwar NNPP, amma suka yi watsi da hakan.

Da suke ƙira ga shugabannin jam’iyyar na gundumomi su tashi tsaye wajen yi wa sabbin mambobi rajista a jam’iyyar ta NNPP, shugabannin sun gargaɗesu da su guji sake yiwa waɗanda aka koran rajista a cikin jam’iyyar.

Taron NNPPn na Ɓilliri, ya samu halartar shugabannin gundumominta 10 dana ƙaramar hukuma da sauran masu ruwa da tsaki.