Daga Yunusa Isa, Gombe
Ɗan Takaran Shugabancin Ƙaramar Hukumar Gombe a zaɓen ƙananan hukumomin daya gabata a Jihar Gombe Hon Adamu Babale Makera da dandazon matasan Jam’iyyar NNPP magoya bayansa, sun bada tabbacin ci gaba da kasancewa a jam’iyyar duk da ficewar tsohon jagoranta Hon. Khamisu Ahmad Mailantarki.
Hon Babale da matasan sun bayyana matsayin nasu ne yayin wani taro da suka yi a Gombe.
Da yake jawabi, jagoran taron kuma ɗan takaran na NNPP zaben ƙananan hukumomin daya gabata a jihar, yace “Duk da cewa mun shigo NNPP ne albarkacin Hon Khamisu Mailantarki, to yanzu dai shi ya fice, kuma muna masa fatan alkhairi, amma mu dai muna nan daram a NNPP, domin mai gida daban, ra’ayi da aƙidar siyasarmu kuma daban. Mu muna da ra’ayi na kashin kanmu”.
Yace yawan sauya sheƙa a tsakanin jam’iyyu lamari ne dake kashe tagomashin siyasar matasa.
Babale Makera ya jawo hankalin matasan su tsaya tsayin daka su kuma jajirce kan aƙida, yana mai shawartar su rika fifita ’yan takara masu nagarta maimakon jam’iyya.
“Duk mutumin da muka gamsu zai iya tsamo mana kitse a wuta to za mu zaɓe shi ko ɗan wacce jam’iyya ce kuwa. Ko jam’iyyar mu ce ta tsaida ɗan takaran da bashi da nagarta to za mu barshi mu bi wadda muke ganin ya fi shi nagarta da armashi. Mun gaji da dodoridon da wasu manya ke yi mana a cikin jam’iyyu, su kai mu su baro”
Ya ƙara da cewa a matsayin su na matasan jam’iyyar NNPP, zasu fito da wata sabuwar tafiya, wacce zata ɗora matasan Gombe kan ingantacciyar turbar siyasa kafin kakar siyasa mai zuwa.
A nata jawabin, ɗaya daga cikin jagororin mata matasa a jam’iyyar ta NNPP, Hajiya Hadiza Muhammad Isma’il, ta ja kunnen mata su guji karɓar ƴan kuɗaɗe, taliya, omo ko turmin zani abunku daga hannun ‘yan siyasa marasa kishi a lokutan zaɓe.
Tace mata ne ke da mafi yawan kuri’u a kowane zaɓe, don haka ya kamata su yi amfani da wannar dama cikin hikima wajen zaɓan shugabanni masu nagarta.