Daga Yunusa Isa, Gombe
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi ƙira da a gyara wassu hanyoyin gwamnatin tarayya da suka haɗe jihohin Arewa Maso Gabas don rage hatsura musamman a waɗannan watanni.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ƙaddamar da gangamin kiyaye hatsura a watannin ƙarshen shekara na bana, tare da taron tattaunawa wadda Hukumar Kiyaye Hatsura ta Ƙasa (FRSC) Reshen Jihar Gombe ta shiryawa masu ruwa da tsaki a Babbar Tashar Mota ta Ibrahim Hassan Dankwambo.
Gwamnan wanda Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri Injiniya Usman Maijama’a Kallamu ya wakilta, yace hanyoyin suna da muhimmanci ga miliyoyin ‘yan Najeriya dake jihohi shida na yankin, kuma sun kasance tamkar gadar dake haɗe yankin da sauran sassan ƙasar nan.
Yace hanyoyin musamman na Gombe zuwa Bauchi, da Gombe zuwa Dukku, da Gombe zuwa Biu, da Gombe zuwa Potiskum da kuma wassu sassan hanyar Gombe zuwa Yola suna ƙara zama tarkon mutuwa ga matafiya musamman a irin waɗannan watanni huɗu na ƙarshen shekara, inda ya yi ƙira ga gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ayyuka ta yi dukkanin mai yiwuwa don daƙile matsalar.
Da yake yabawa hukumar ta FRSC bisa jajircewarta wajen rage hatsura, gwamnan yace gwamnatinsa ta cimma nasarar fiye da kaso 70 cikin 100 a shirinta na Network Eleven Hundred, inda ake yiwa kowace ƙaramar hukuma hanyoyi aƙalla kilomita 100-100 don inganta zirga-zirga tsakanin birane da yankunan karkara.
Da yake magana kan taken gangamin magance hatsuran na bana; wato “Yi Magana Kan Tuƙin Ganganci: Hatsura Suna Kashe Fasinjoji Fiye da Direbobi”, Gwamnan ya buƙaci fasinjojin su riƙa sanya ido kan direbobi a yayin tuƙi.
A jawabinsa na maraba, Kwamandan Hukumar ta FRSC a Jihar Gombe Samson Ƙaura, yace hukumar ta ɓullo da sabbin dabaru don ganin an rage yawan hatsura a hanyoyin ƙasar nan.
Ya kuma yi kira ga direbobi su riƙe amanar fasinjoji, ta hanyar tabbatar da cewa motocinsu suna da lafiya, su guji shan giya ko ƙwaya kafin ko a lokacin tuƙi, kana su kasance masu bin dokoki da ƙa’idojin hanya.
Ƙaura ya ja hankalin fasinjoji su kai rahoton duk wani direban dake tuƙin ganganci ga ofishin hukumar ta FRSC mafi kusa ko wata hukumar tsaro data dace.
A nasa jawabin Babban Manajan Kamfanin Sufuri na Jihar Gombe da aka fi sani da Gombe Line, Dr Sani Sabo, ya jaddada ƙira ga Gwamnatin Tarayya kan ta gaggauta gyara hanyoyin na jihohin Arewa Maso Gabas don ceto rayukan direbobi dana fasinjoji.
Ya kuma yabawa gwamnatin jihar da hukumar ta FRSC da sauran masu ruwa da tsaki bisa jajircewar da suke yi na rage yawan hatsura a kan hanyoyin Jihar Gombe dana ƙasa baki ɗaya.
A saƙonninsu fatan alheri, wakilan hukumomin tsaro daban-daban, da shugabannin ƙungiyoyin sufuri, da sarakunan gargajiya, sun yabawa hukumar kiyaye hatsuran bisa jajircewarta kan rage hatsura, suna masu ƙira ga direbobi da fasinjoji su riƙa bin ƙa’idojin tafiye-tafiye.