…Labarin Wani Uba Mai Lalata Da Ƴarsa A Jihar Gombe

 

Rubutawar Comfort Mukollo, Gombe

 

A wani ƙauye mai nisa da ake ƙira Chamchiyo dake Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe ta Najeriya, wata yarinya ƴar shekaru 15 mai suna Chayilo ta shafe shekaru da dama tana rayuwa cikin ƙuncin cutarwa da cin zarafi, inda mijin mahaifiyarta ke lalata da ita akai-akai har ya maida ita tamkar wata kuyanga.

 

Yayinda ta shaidawa mahaifiyarta wannan lamari, sai mahaifiyar ta hau ta da faɗa da zagi, wai tana zargin mijinta da irin wannan mugun aiki, haka Chayilo ta yi haƙurin dole ƙunshe da wannan ƙunci da takaici, yayin da mahaifiyar tata ta yi ko oho da ita.

 

Wannan yanayi ya kaita ga daina sha’awar zuwa makaranta da shiga tarukan jama’a. Ƙawayenta sun lura da hakan, musamman yadda take fashin zuwa makaranta tare da ƙaurace musu. Sun yi ta ƙoƙarin gano dalilinta na wannan sauyi, amma Chayilo ta ƙi cewa komai.

 

Irin wannan lamari ba Chayilo kaɗai yake shafa ba; dubban mata da ‘yan mata a faɗin Najeriya suna fama da makamancin wannan ƙunci ba tare da kowa ya sani ba. Da dama sun zaɓi su yi shiru saboda tsoro, kunya, da fargabar abinda ka je ya zo.

 

Sai dai rayuwar Chayilo ta ɗauki wani sabon salo yayinda tawagar ƴan sa kai waɗanda ƙungiyar kare haƙƙi da muradun mata ta WRAPA reshen Jihar Gombe ta dira a Karamar Hukumar Balanga. Wannar ƙungiya wata ɓangare ce ta wani babban gangami wadda gwamnati, da ƙungiyoyin addini dana fararen fula, da sarakuna, da sauran masu ruwa da tsaki suke marawa baya don magance matsalar cin zarafin mata data addabi al’umma.

 

Masu aikin sa kan waɗanda galibinsu mata ne, an ba su horo da ilimin ganowa da tallafawa waɗanda aka ciwa zarafi. Sukan bi gida-gida suna tattaunawa da mata cikin sirri, suna sauraron koke-kokensu, da basu shawarwari da ƙarfafa musu gwiwa dama tallafa musu. Ganin ta fara hango haske da alamun nasara, Chayilo ta saki jikinta, a hankali ta fara bayyana abubuwan da suka faru da ita.

 

Ƴan sa kan sun haɗa Chayilo da wata ƙungiyar tallafi ta yankin, inda ta haɗu da wassu matan da suma suka fuskanci makamancin wannan tashin hankali na cin zarafi a rayuwa. Sun yi ta baiwa juna labarun abubuwan da suka faru da su, suna samun sauƙi da kwanciyar hankali a tsakaninsu, lamarin da ya kaisu ga fara samun waraka daga halin da suke ciki. Chayilo ta kuma samu shawarwari da tallafin likitoci sakamakon haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin na sa-kai da ma’aikatan lafiya na yankin.

 

Labarin Chayilo ɗaya ne daga cikin ire-irensa da dama da suka fara bayyana, yayin da ƙoƙarin haɗin gwiwa kan yaƙi da cin zarafin mata ke ƙara karfi. masu ruwa da tsaki daban-daban suna aiki tuƙuru don samar da al’ummar da mata da ƴan mata za su rayu ba tare da fargabar cin zarafi ba.

 

Chayilo tace “Da ina cikin duhu, amma WRAPA ta haskaka min rayuwata”, ta faɗi hakan idanuwanta cike da ƙwalla. Ta ƙara da cewa “Sun ba ni ƙwarin gwiwar yin magana da neman taimako. Ina matuƙar godiya a gare su har abada.”

 

Ko’odinetar ƙungiyar ta WRAPA a Jihar Gombe, Misis Anita Dogo, tace lallai lamarin Chayilo abin tausayi ne, hakan ya sa WRAPA ta kai mata ɗaukin gaggawa don ceto rayuwarta kafin ya ta’azzara. A cewarta, “Na hango haske a rayuwarta, kuma na ga akwai buƙatar kyautata makoma da lafiya da tunaninta”.

 

Ɗaya daga cikin muhimman matakan da aka ɗauka shi ne kafa Ma’aikatar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Gombe, wacce take namijin ƙoƙari wajen ganin an inganta rayuwar mata da magance cin zarafinsu.

Kwamishinar mata da bunƙasa walwalar al’umma ta Jihar Gombe Hon. Asamau Iganus, tace gwamnatin Jihar Gombe ta zartar da dokar magance cin zarafin jama’a ta (VAPP) don samar da cikakken tsarin rigakafi da magance cin zarafin mata da ƴan mata.

 

Tace labarin Chayilo dake cike da ban tausayi, yana ɗaya daga cikin matsalolin da mata da ‘yan mata ke fuskanta a kullum.

“Na yi matuƙar farin ciki da aka amince da wannar doka ta VAPP domin zata kare mata da ƴan mata dama tabbtar da yi musu adalci”.

 

Gwamnati ta samar da cibiyar kula da waɗanda aka ci wa zarafi a ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta Jihar Gombe don bada tallafi da rigakafin magance cin zarafin mata.

 

Ma’aikatar tana aiki kafaɗa da kafaɗa da ma’aikatar lafiya, da ƙungiyoyi masu zaman kansu don ayyukansu na bada tallafi da shawarwari, da bada mafaka, da taimako ta fuskar shari’a ga waɗanda suka fuskanci cin zarafi.

 

Wani ƙoƙarin kuma da gwamnati ta yi, shi ne kafa cibiyar kula da waɗanda aka ciwa zarafi a Asibitin Ƙwararru na Gombe inda ake samun rahotannin fyaɗe da sauransu.

 

Haka kuma Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya dake Gombe, ya kafa kwamitin yaƙi da cin zarafin mata, da kuma tawagar bada tallafi ga waɗanda aka ciwa zarafi. Har ila yau, asibitin yana da wani tsari na musamman don kula da lamuran cin zarafi.

 

Wata babbar jigo kuma ita ce ƙungiyar mata ta ƙasa (NCWS) reshen Jihar Gombe, wacce ke fafutukar kare haƙƙin mata da bada tallafi ga waɗanda aka ciwa zarafi.

Shugabar Kungiyar ta NCWS ta Jihar Gombe Hajiya Hauwa Saraki, tace ƙungiyar tana karɓa tare da kula da koke-koken cin zarafin mata da ƴan mata, tana mai cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba har sai an samu raguwar cin zarafin mata.

 

Haka kuma gwamnatin Jihar Gombe ta haɗa hannu da ƙungiyoyi masu zaman kansu kamar su ƙungiyar kare yanci da muradun mata ta WRAPA, da ƙungiyar lauyoyi mata ta ƙasa da ƙasa (FIDA) don bada horo da tallafi ga jami’an tsaro da alƙalai da sauran masu ruwa da tsaki kan yaƙi da cin zarafin mata.

 

A Jihar Gombe, sarakuna da malaman addini suna da tasiri matuƙa, kuma maganganu da ayyukansu suna tasiri sosai ga jama’arsu.

 

Babban basaraken dake gaba-gaba a ƙoƙarin magance cin zarafin mata da ƴan mata shi ne Mai Martaba Sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar na 3. Sarkin ya kasance mai fafutukar kare haƙƙin mata, kuma ya na ƙoƙarin inganta ilimi da ƙarfafa tattalin arziƙin mata da ƴan mata.

Yace “Dole ne mu gane cewa cin zarafin mata da ‘yan mata ba batun mata ba ne kawai, batu ne na kare haƙƙin bil’adama,” Sarkin ya shaidawa manema labarai a wata hira cewa “Dole ne mu haɗa kai don samar da al’ummar da mata da ƴan mata za su rayu ba tare da fargabar tashin hankali, cin zarafi ko wariya ba.”

 

Sakataren Jama’atu Nasril Islam na Jihar Gombe Alhaji Saleh Damburam da Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen Jihar Gombe Reverend Father Joseph Alphonsus Shinga, sun ƙarfafa kalaman sarkin, wadanda suka duƙufa wajen inganta ‘yancin mata da ƙalubalantar al’adu masu cutarwa.

 

“Musulunci da Kiristanci sun koyar da mu mutuntawa da kare haƙƙin mata da ƴan mata,” in ji su. “Dole ne mu yi aiki don inganta ilimi da ƙarfafa tattalin arziƙin mata da ƴan mata, mu kuma ƙalubalanci halaye da dabi’un dake haifar da tayar da hankali, cin zarafi da kuma wariya ga mata.

 

Yanzu haka dai a ƙoƙarin da ƙungiyar ta WRAPA ke yi, wani lauya ya ɗaura ɗamarar ganin an yi wa Chayilo adalci, inda aka kamo wanda ya aikata laifin, aka gurfanar da shi a gaban kotu, yanzu haka yana gidan yari bayan daya amsa laifinsa.

 

Mahaifiyar Chayilo ta cika da baƙin cikin rashin amincewa da bayanan ƴarta tun farko, har ya kai ga ta jefa ta cikin hatsari.

 

A ƙoƙarinta na kawo ƙarshen cin zarafin mata a Jihar Gombe, gwamnatin jihar ta ƙarfafa jami’ai da hukumomin tsaro don ganin an aiwatar da dokar ta VAPP.

 

Tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin fararen fula dana al’umma, gwamnatin tana shirya gangamin wayar da kan al’umma akai-akai, da tarurrukan bita don canza ɗabi’u da tunanin jama’a, da kafa matsuguni da cibiyar bada shawara da shirye-shiryen tallafi.

 

Gwamnatin takan kuma shirya taruka wa sarakuna da shugabannin addini don haɓaka kyawawan al’adu da ɗabi’u, da kuma inganta damawa da mata a harkokin mulki da tattalin arziki.

 

An kafa ƙungiyoyin jin ƙai masu yaki da cin zarafin jinsi (GBV), da horar da ma’aikatan kiwon lafiya, da jami’an kyautata zamantakewa, da jami’an tsaro don bada gudunmawa yadda ya kamata, tare da gudanar da bincike don tattara bayanai kan magance matsalolin cin zarafin jinsi da sauran abubuwan dake faruwa a Jihar Gombe.

 

Gwamnatin takan kuma yi haɗin gwiwa da ƙungiyoyin cikin gida dana ƙasa da ƙasa don samarwa da aiwatar da manufofin magance cin zarafin jinsi a wuraren aiki, da makarantu da kuma a cikina l’umma.

 

Lamari ya kawo ƙarshen aurenta da wannan mutumin da ya yi ta cin zarafin Chayilo.

 

Komin tsanani dai akwai fatan sauƙi. Yunkurin da gwamnati da ƙungiyoyin addini dana fararen fula da sarakuna da masu ruwa da tsaki ke yi na magance matsalar cin zarafin mata da ƴan mata a jihar Gombe ya fara yin tasiri tare da haifar da ɗa mai ido.

 

Zai yi wuya dai a iya kawo ƙarshen cin zarafin mata da ƴan mata a Jihar Gombe nan kusa, amma a bayyane yake cewa ana samun ci gaba.

 

Har yanzu da sauran aiki da yawa a gaba. Dole ne mu ci gaba da tallafawa waɗanda suka tsira daga tashin hankali na cin zarafi, da haɓaka ilimi da ƙarfafa tattalin arziƙin mata da ƴan mata, tare da ƙalubalantar halaye da ɗabi’un dake haifar da cin zarafi da wariya.

 

Ta haka ne kawai za mu iya samar da al’ummar da mata da ƴan mata za su rayu ba tare da fargaba ko tsoron cin zarafi da wariya ba, domin su kai ga gaci na cimma muradu da burukan rayuwarsu.

 

Comfort Mukullo, ƴar jarida ce mai fafutukar ci gaba a Jihar Gombe.