Daga Yunusa Isa, Gombe
Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta Jihar Gombe ta karɓi buƙatun kamfanonin kwangila guda bakwai, waɗanda ke neman ayyukan gina sabin cibiyoyin rukunan gwamnati uku, da suka haɗa da Majalisar Dokokin Jiha, da Rukunin ɓangaren Shari’a da kuma Sakatariyar Jiha.
Da yake jawabi yayin bikin miƙa buƙatun kamfanonin a ma’aikatar, Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri Injiniya Usman Maijama’a Kallamu ya tabbatarwa ‘yan kwangilan aniyar ma’aikatar na yin adalci da daidaito wajen nazarin buƙatun da suka gabatar kafin zaɓan waɗanda zasu yi nasara.
Maijama’a wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren Ma’aikatar Idris Yanbiyu Buba, ya buƙaci duk ‘yan kwangilan da suka yi nasara su tsaya kan ka’idojin kwangilolin, tare da kammala su akan lokaci.
Ya kuma yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa hangen nesansa na gina cibiyoyin rukunan gwamnatin uku, yana mai cewa idan aka kammalasu, Gombe za ta kasance tauraruwar jiha wacce za a yi ta koyi da ita a ƙasar nan.
Tun farko a nasu jawaban, wakilan ’yan kwangila, dana ƙungiyoyin fararen fula, da wakilin ofishin bin ka’idoji a harkokin gwamnati, da kuma Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar kan Ayyuka na Musamman Architect Yakubu Mamman, sun yaba da tsarin neman kwangilolin, suna masu bayyana shi a matsayin wadda aka yi cikin gaskiya da adalci.
Suka ce ba za ce ga wadda ya yi asara ba a ƙarshen lamarin, saboda ’yan kwangila suna ɗaukar kansu a matsayin iyali guda.
Sun yabawa ma’aikatar ayyukan bisa yadda a kullum take bin tsari a harkokinta yadda ya dace, suna masu ƙira ga sauran ma’aikatu su yi koyi da ita.
Kamfanonin bakwai da suka gabatar da bukatun su na yin ayyukan uku sune: KIPS ENGINEERING LTD, da TERN GLOBAL, da KASH CONSTRUCTION NIG LTD, da BMC, da A&K NIG LTD, da SUJECT CONSTRUCTION NIG LTD, da kuma UTMOST NIG LTD.