Daga Yunusa Isa, Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe ta baiwa al’ummar Jihar tabbacin ci gaba da samar da magunguna masu inganci da rahusa a dukkan asibitoci matakin farko dake gundumomi 114 na jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Habu Ɗahiru ne ya bada tabbacin hakan yayin daya ƙaddamar da taron horaswa da wayar da kan shuwagabannin asibitoci matakin farko na jihar, a asibitin kwararru na jihar.

Dr Habu Ɗahiru yace “Ma’aikatan lafiya sune ƙashin bayan aikin jinya, don haka suna buƙatar ƙarin masaniya kan sabin dabaru da tsare-tsaren sarrafa magunguna don amfanin majinyata”.

Ya buƙaci mahalarta taron su nazarci sabon tsarin sarrafa magungunan cikin tsanaki, don marasa lafiya su samu nagartacciya kiwon lafiya ta zamani.

A nasa ɓangaren, Babban Sakataren Hukumar Kula da Magunguna da kayayyakin jinyan ta Jihar Gombe (GODMA) Pharmacist Caleb Faransa, yace “Duk magungunan da ake kawowa Jihar Gombe sai an yi musu gwaji a dakin gwaje-gwajen da muka tanadar don tabbatar da sahihanci da ingancinsu, don tabbatar da cewa al’ummarmu suna shan lafiyayyun kwayoyi da magunguna.

Babban Sakataren yace dukkanin manyan asibitoci da waɗanda ake kira cottage hospitals guda 24 a jihar cike suke da ingantattun magunguna masu rahusa don kula da marasa lafiya.

Kwamishinan lafiya da sakataren hukumar sun yabawa gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya bisa ƙoƙarinsa na samar da sabbin tsare-tsare da zamanantar da fannin kiwon lafiyan jihar ya zuwa na zamani a jihar.

Wasu mahalarta taron da suka zanta da manema labarai, sun yabawa hukumar ta GODMA da Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Jiha bisa shirya irin wannan muhimmin horon, suna bada tabbacin cewa horon zai taimaka musu wajen fahimtar tsarin sarrafa magungunan na zamani.