A wani mataki na daƙile ƙalubalen tattalin arziƙin da al’ummar Jihar Gombe ke fuskanta a halin yanzu, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya amince da raba kayan abinci ga marassa galihu a faɗin jihar.

 

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Ismaila Uba Misilli ya fitar tare da miƙawa Jewel Times Hausa.

 

Misilli yace hakan na zuwa ne bayan ƙudurin hakan da aka cimma a babban taron majalisar tsaron jihar da Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranta jiya Litinin.

 

Don haka Gwamnan ya amince da raba buhunan dawa dubu masu nauyin kilogiram 50-50 da buhunan shinkafa dubu masu nauyin kilogiram 25 da katon dubu na taliya ga kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 11 na Jihar Gombe.

 

Hakazalika, za a raba irin wannan tallafin abinci, buhuna 5,000 da katon-katon na taliya ga ƙungiyoyin addini, da ƙungiyoyin fararen hula, da ƙungiyoyin ɗalibai (GOSSA da NANS), da makarantun tsangaya da almajirai, da ƙungiyoyin matasa da mata da kuma masu buƙata ta musamman da sauran jama’a masu rauni a cikin al’umma.

 

Wannan dai shi ne karo na 19 da gwamnatin za ta raba irin wannan tallafi ga al’ummar Jihar Gombe a ci gaba da ƙoƙarin samar da agaji da inganta rayuwar al’ummar jihar a wannan mawuyacin lokaci.

 

Ana sa ran tallafin abincin zai taimaka matuƙa wajen rage wahalhalun da jama’a da dama ke fama da su a jihar, musamman ma masu rauni.

 

Gwamna Inuwa Yahaya, ya ƙara jajircewa wajen aiwatar da ingantattun matakan tallafawa jama’a don sauƙaƙa musu rayuwa a tsaka da fama da ƙalubalen tattalin arziƙin da ake ciki.