Daga Yunusa Isa, Gombe
Hukumar Kula da Magunguna da kayayyakin jinya ta Jihar Gombe (GODMA) tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, ta shirya taron yini biyu ga kwamitin kula da tsarin samar da magunguna da kayayyakin jinya wa Jihar, don tabbatar da samar da ingantattun magunguna da kayayyakin jinya a ɗokacin asibitocin jihar.
Da yake jawabi yayin kaddamar da taron jiya Laraba a hotel din Eeman, kwamishinan lafiya na jihar Dr Habu Ɗahiru yace horon yana daga cikin ƙudurorin da gwamnatin jihar na samar da tsarin kiwon lafiya mai rahusa ga kowa.
Dokta Ɗahiru wanda Babban Sakataren ma’aikatar Muhammad Ibrahim Jalo ya wakilta, yace horon zai baiwa mahalarta taron sanin makama, kan yadda za su tabbatar da samar da magunguna da kayayyakin ba tare da tangarda ba ga jihar.
A jawabinsa na maraba, Babban Sakataren Hukumar samar da Magunguna da kayayyakin jinya ta Jihar (GODMA) Pharmacist Caleb Faransa, yace horon zai karawa ‘yan kwamitin sanin makamar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Yace an gayyaci ƙwararrun masana don baiwa mahalartan horon bunkasa dabarun zamani na samarwa da kula da magunguna da tsarin samar da kayayyakin jinya.
Caleb Faransa ya ba da tabbacin cewa, da zuwan hukumar ta GODMA, karancin magunguna wadda ya kasance daga cikin matsalolin da suka gurgunta asibitocin jihar a baya, yanzu ya zama tarihi.
A sakonsu na fatan alheri, wakilai daga hukumomin lafiya da jami’an ma’aikatar lafiya da kuma abokan huldar ci gaba sun yabawa hukumar ta GODMA bisa wannan shiri, suna masu bayyana fatan cewa duba da dabarun da hukumar ta bullo da su, za a samar da magunguna da kayayyakin jinya a jihar yadda ya kamata.
Jim kadan bayan kaddamarwar aka fara taron bitar gadan-gadan