Daga Christopher Joshua, Kaltungo
Saminu Eli karamin yaro ne ɗan Garin Kaltungo wanda aka gano yana ɗauke da cutar ciwon ciki na hernia. Bayan da aka gano cutar, likitoci sunyi gaggawar kawo masa ɗauki inda akayi nasarar yi masa tiyata.
Mahaifiyarsa Esther Eli da take cike da farin ciki ta bayyana irin sa’ar da suka taka saboda shigar da yaron cikin tsarin GoHealth.
“N510 kawai muka biya – wanda shine kashi 10% na magunguna”, Mis Eli ta faɗa yayin da take bayyana alfanun da ta samu.
“Lokacin da aka shawarceni da na yi rajista ƙarƙashin tsarin GoHealth, sai na yi tunanin abu ne na siyasa kawai, muka ƙi rajista, sai a ‘yan watannin da suka gabata na kai yarona asibiti, saboda ya yi fama da zazzabin taifot da zazzabin cizon sauro kuma mun kashe sama da Naira 10,000 wajen jinyar sa.
“Daga nan sai muka yi magana da ɗaya daga cikin abokan aiki na, kuma ya shawarce ni da in yiwa ‘ya’yana rajista cikin tsarin, sai na gamsu kuma na yi musu rajista. Daga nan ne na fara amfana da ayyukan da GoHealth ke samarwa da ni da ‘ya’ya na, ciki har da Saminu.”
Mis Eli ta ƙara da cewa GoHealth na ɗaya daga cikin ayyukan alkhairi da manufofin Mai Girma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya kawo da suke shafar ma’aikatan gwamnati da talakawa kai tsaye.
“Gaskiya, GoHealth kyakkyawan tsari ne da ke matukar taimakawa ma’aikata dama ɗaukacin al’ummar Jihar Gombe”
GoHealth dai tsari ne na taimakekeniyar lafiya da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya ƙirƙira domin samar da kiwon lafiya mai inganci da rahusa ga dukkan al’ummar Jihar Gombe.