Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya amince da bada tallafin Naira 500,000 ga kowane mahajjacin jihar daga cikin maniyata 1273 da za su yi aikin Hajjin bana.
Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa da
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Ismaila Uba Misilli ya fitar tare da miƙa ta ga Jewel Times Hausa yau Juma’a.
Sanarwar tace amincewar ta zo ne biyo bayan sanarwar da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta fitar a baya-bayan nan game da sauye-sauyen da aka samu a kuɗin Hajjin bana.
Yace an bada tallafin ne don rage raɗaɗin kuɗi da alhazan Jihar Gomben ke fama da shi a halin yanzu.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi fatan wannan tallafi zai taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin bana cikin tsanaki, tare da inganta jin daɗin maniyyatan Jihar Gombe dama samar musu yanayi mai kyau na gudanar da ayyukan addini duk da ƙalubalen tattalin arziƙi da ake fama da shi.